Featured
Hatsarin Tankar Gas Ya Yi Ajalin Mutum 12 A Imo

Wata tankar gas ta yi karo da mota a kan hanyar Owerri–Onitsha Expressway da ke Jihar Imo, inda mutum 12 suka rasa rayukansu, ciki har da yara hudu da kuma manyan mutane takwas, kamar yadda gidan talabijin Channels ya ruwaito.
Kwamishinan ƴan sanda na Jihar Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa wasu mutum takwas sun jikkata, kuma a halin yanzu suna karɓar kulawa a asibiti.
Rundunar ƴan sanda ta ce ta kaddamar da bincike kan musabbabin hatsarin, yayin da aka ci gaba da zirga-zirga a titin bayan an share tarkacen da ya taru a wurin.
Kwamishinan ƴan sanda, Aboki Danjuma, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan, tare da yin gargadi ga direbobi da su guji tuƙi a hanyoyi ta hanyar da ba ta dace ba, domin kare rayuka da dukiyoyi.