Addini
Gwamnatin Kano Ta Ayyana Juma’a a Matsayin Ranar Hutun Mauludi

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Juma’a, 12 ga Satumba, 2025, a matsayin ranar hutu domin bikin Maulud, wato ranar tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Wannan ya zo daidai da 19 ga Rabi’ul Awwal, 1447 AH a kalandar Musulunci.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, inda ya bayyana cewa hutun ya biyo bayan muhimmancin Maulud a matsayin lokaci na ibada, tunani da nuni ga koyarwar Manzon Allah (SAW).
Gwamnatin ta bukaci ma’aikata, ‘yan kasuwa da sauran jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin tunani kan darussan haɗin kai, hakuri da kuma bin doka da oda. Haka kuma ta shawarci jama’a da su zauna cikin kwanciyar hankali da lumana.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta yi kira ga al’umma da su yi addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya da ci gaban jihar da Najeriya baki ɗaya, tare da taya al’ummar Kano murnar bikin Maulud mai albarka.