Connect with us

Featured

Farashin Kayan Abinci Yayi Rugu-Rugu A Najeriya – Ministan Noma

Ministan Noma a Najeriya Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana cewa farashin kayan abinci ya ragu a fadin Najeriya, sakamakon matakan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɗauka. Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a tashar ARISE TV a ranar Juma’a12 ga Satumba, 2025. Inda ya ce dabarun gwamnatin sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Kyari ya bayyana cewa Tinubu ya gaji ƙalubale mai tsanani a fannin samar da abinci, lamarin da ya sa ya ayyana dokar ta-baci kan abinci tun watan Yuli 2023. Ya ce matakan sun haɗa da ƙarfafa manoma da kuma buɗe ɗan lokaci na shigo da wasu kayayyakin abinci domin cike gibin da ake da shi, musamman a fannin shinkafa da wasu muhimman kayan abinci.

Ya ce shigo da kayan abinci na wucin gadi bai yi nisa ba amma har ya gajiyar da manoma, domin an ware shi na watanni shida kacal. A lokaci guda kuwa, gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin taki har buhunan miliyan biyu ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN), tare da rangwamen kashi 50% don ƙarfafa samarwa.

Ministan ya jaddada cewa wadannan matakai sun taimaka wajen kara yawan noma a shekarar 2024, abin da ya taimaka aka samu raguwar tsadar abinci da kara wadatar kayayyaki a kasuwa. Haka kuma Shugaba Tinubu ya kafa kwamiti na majalisar zartarwa domin sa ido a kan farashin abinci a fadin kasar nan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetmatbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet