Featured
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Aniyarta Na Yin Aiki Tare Da Ƙungiyoyin Fararen Hula
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yin aiki tare da kungiyoyin fararen hula domin tsara manufofi, sa ido kan ayyuka da kuma karfafa tattaunawa da jama’a don samar da ci gaban jihar. Ya bayyana haka ne a taron kwanaki biyu da Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida ta shirya a ranar Litinin 15 ga Satumba, a Jami’ar Khairunda ke Kano, inda ya ce ƙungiyoyin fararen hula na da muhimmanci wajen cike gibi tsakanin shirye-shiryen gwamnati da bukatun al’umma.
Gwamnan, wanda Mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta, ya bukaci mahalarta taron su mayar da hankali kan karfafa kungiyoyi, karfafa hadin kai tsakanin gwamnati, ‘yan kasuwa da al’umma, amfani da fasaha wajen karfafa tattaunawa, tallafawa matasa da kuma kara juriya a wuraren da ke da rauni. Ya kuma bayyana kungiyoyi masu zaman kansu a matsayin ginshikan ci gaban ilimi, kiwon lafiya, adalcin jinsi, kare muhalli, yaki da rashawa da warware rikice-rikice.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana taron wanda shi ne irinsa na farko a Kano a matsayin sabon babi na gaskiya da ci gaban al’umma daga tushe. Ya ce gwamnatin Abba Yusuf ta aiwatar da sauye-sauye bisa dokar saye da sayar da kayayyakin gwamnati da aka gyara domin tabbatar da ingantaccen aiki, kiyaye kudi da kuma kara amincewar jama’a.
