Connect with us

Featured

Sama Da Ƴan Najeriya Miliyan 123 Sun Mallaki Shaidar NIN – NIMC

Hukumar Kula da Shaidar Zamantakewa ta Ƙasa (NIMC) ta bayyana cewa fiye da ‘yan Najeriya miliyan 123 sun riga sun shiga cikin kundin bayanan shaida na ƙasa. Darakta-Janar na NIMC, Abisoye Coker-Odusote, ta ce wannan cigaba ya sa an samu damar rage lokacin jira da kashi 49 bisa ɗari sakamakon sabbin fasahohi da haɗin gwiwa da hukumomi daban-daban. Ta kuma ce an shigar da fiye da kashi 75 cikin 100 na fursunoni a tsarin.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce shirin shaida na ƙasa ba wai fasaha ce kawai ba, har ma lamari ne na gudanar da mulki da inganta sahihancin ƙasar a idon duniya. Ya jaddada muhimmancin gaskiya a saye da sayarwa, gwaji na dindindin da bin ka’idojin duniya domin tabbatar da amincin bayanai da kuma sahihancin takardun shaida na Najeriya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ya wakilta, ya ce NIN shi ne mabuɗin samun kowane irin sabis a ɓangaren gwamnati da na masu zaman kansu. Ya bayyana cewa shirin yana da muhimmanci wajen tsaro, bunƙasa tattalin arziki da kuma bai wa ‘yan ƙasa damar shiga duniyar dijital yadda ya kamata.

Tinubu ya kuma yi kira ga hukumomin gwamnati su haɗa kai, tare da karfafa haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu da abokan hulɗar ƙasashen waje.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet