Connect with us

Featured

Dubban Falasɗinawa Na Tserewa Daga Gaza Sakamako Ƙaruwar Hare-haren Isra’ila

Dubban Falasdinawa na ci gaba da tserewa daga birnin Gaza, kwana guda bayan Isra’ila ta fara kai farmaki ta ƙasa a wani yunkuri na murkushe mayaƙan Hamas. Shaidu sun bayyana cewa, mafi yawan waɗanda ke tserewa sun nufi kudancin Gaza a kafa domin neman mafaka daga hare-haren.

Kungiyoyin agaji fiye da 20 da ke aiki a yankin, ciki har da Save the Children da Oxfam, sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka bayyana cewa halin rashin imani da ake ciki a Gaza ya ƙara tsananta. Kungiyoyin sun gargadi cewa, talauci, yunwa da rashin magunguna na iya jefa miliyoyin mutane cikin bala’i.

Rahotanni sun ce jama’a na fama da matsalar wutar lantarki da ƙarancin ruwan sha, yayin da gidaje da dama ke cigaba da rushewa sakamakon hare-haren. Masu tserewar sun ce babu inda suka nufa face wani ɓangare na kudancin Gaza wanda su ma ake ci gaba da kai hari akai-akai.

A mako mai zuwa ne shugabannin kasashen duniya za su tattauna game da rikicin Gaza a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ake sa ran za a samar da matakan gaggawa na kawo ƙarshen tashin-tashina da ceto rayukan fararen hula.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet sssjojobet güvenlikjojobet güvenlikjojobetholiganbetholiganbetjojobetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetjojobet erişimgrandpashabetjojobetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişDeneme Bonusujojobetjojobetjojobet