Connect with us

Featured

Ibas Ya Ƙalubalanci Binciken Majalisar Dokokin Jihar Rivers Kan Kuɗi Naira Biliyan 254 A Wa’adin Mulkinsa

Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta ce za ta binciki yadda aka kashe kudaden shiga na watanni shida da suka gabata a lokacin mulkin tsohon shugaban riƙo na Jihar, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (rtd.). Majalisar, karkashin jagorancin Kakakin ta, Martin Amaewhule, ta ce za ta binciki yadda aka yi amfani da kudaden asusun gwamnati da bayar da kwangiloli a lokacin dokar ta-baci. Rahotanni sun nuna cewa Rivers ta samu fiye da N254bn daga kudaden tarayya (FAAC) tsakanin watan Maris da Agusta 2025, mafi yawan kudin an same su ne daga kaso 13% na harajin man fetur.

Sai dai tsohon shugaban riko na jihar, Ibas, ya yi watsi da wannan mataki na Majalisar, yana mai cewa ba ta da hurumin bincikensa domin ba su ne suka nada shi ba. Ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Hector Igbikiowubu, Ibas ya bayyana binciken da Majalisar ta shirya a matsayin “yunkuri na banza,” yana mai cewa ya yi aiki ne a madadin Shugaban kasa kuma karkashin kulawar Majalisar Dattijai da ta Tarayya.

Ibas ya ce ko-da-yake Majalisar na iya binciken ayyukan da ta dauka a matsayin nata nauyi, amma ba ta da ikon tambayarsa kai tsaye. Ya ce kowane irin bincike kan ayyukansa zai zama kamar binciken Shugaban kasa da kuma Majalisar Tarayya wadda ta kula da ayyukansa. Wannan dai na zuwa ne yayin da kungiyoyi da jam’iyyun adawa suka fara kira da a binciki yadda aka gudanar da kudaden Jihar a lokacin mulkin rikon kwarya.

A gefe guda kuma, Gwamna Siminalayi Fubara ya koma bakin aiki bayan karewar dokar ta-baci, inda ya bukaci al’ummar Jihar su ci gaba da yi masa addu’a domin samun nasara wajen gudanar da mulki. A jawabinsa a cocin St. Paul’s Anglican Church da ke Opobo, Fubara ya gode wa jama’a bisa addu’o’in da suka yi masa, yana mai cewa hakan ya ba shi karfin guiwa, tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya don ci gaban Jihar Rivers.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet