Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Za Ta Taƙaita Kashe Kuɗi Yayin Bikin Cikar Najeriya Shekaru 65 – Muhammad Idris

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta gudanar da bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a cikin salo na takaita kashe kudi. Ministan Yaɗa Labarai nanƘasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na musamman kafin bikin ranar ‘yancin kai da aka gudanar a Abuja. Ya ce taken bikin na bana shi ne “All Hands on Deck”, inda aka fara da sallar Jumu’a a ranar Juma’a da kuma addu’ar godiya a ranar Lahadi.

Bikin ya kuma haɗa da gasar muhawarar ɗalibai ta ƙasa baki ɗaya a matsayin wani muhimmin ɓangare na tunawa da wannan rana mai tarihi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnati ke ƙoƙarin jaddada muhimmancin haɗin kai da ƙarfafa zumunci tsakanin ‘yan ƙasa.

Haka kuma Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) ta gabatar da “National Value Charter” wanda ke nufin ƙarfafa kaunar ƙasa da ɗabi’un kirki ta hanyar bayyana alkawarin gwamnati ga ‘yan ƙasa da kuma abin da ake tsammani daga al’umma. Wannan ya ƙunshi “Nigerian Promise” wanda ya fayyace jajircewar gwamnati wajen kare ‘yanci, daidaito, zaman lafiya, haɗin kai da walwalar tattalin arziki.

A gefe guda kuma, an samar da “Citizen’s Code” don karfafa wa ‘yan ƙasa irin dabi’un da suka haɗa da ladabi, ɗabi’ar kulawa da juna, juriya, gaskiya, nagartaccen shugabanci, kulawa da muhalli, da kuma hakuri. Hukumar NOA ta ce za ta ci gaba da yada waɗannan manufofi ta hanyar wayar da kai, haɗin gwiwa da al’umma, da amfani da kafafen sada zumunta domin gina ƙasa mai nagarta.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet