Connect with us

Addini

Kungiyar Ahlussunnah Ta Buƙaci Gwamnatin Kano Ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Abduljabbar

Kungiyar Ahlussunnah Wal-Jama’ah ta Jihar Kano ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta nisanci siyasantar da shari’ar Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara, wanda aka samu da laifin batanci ga Annabi Muhammad (SAW). Kungiyar ta bayyana haka ne a taron manema labarai da ta gudanar a Markaz Imamul Bukhari, Rijiyar Zaki, Kano, a karkashin jagorancin Farfesa Muhammad Muslim Ibrahim.

Kungiyar ta ce ta kira taron ne domin mayar da martani kan kalaman Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya yi a wurin Mauludi a Turasul Islam Jumu’a Mosque, Gwale, inda ya yi ikirarin cewa hukuncin da aka yanke wa Abduljabbar siyasa ce ta kawo shi. Kungiyar ta ce irin wannan magana tana iya tada fitina da kuma haifar da shakku a zukatan jama’a kan gaskiyar shari’ar da aka gudanar.

Kungiyar ta nanata cewa Abduljabbar ya yi furuci na batanci a fili, an kuma ba shi damar kare kansa tare da wakilai na shari’a da kuma dama mai yawa ta gabatar da hujjoji a gaban kotun Shari’a. Saboda haka hukuncin da aka yanke masa ya kasance bisa gaskiya ne ba siyasa ba. Kungiyar ta yi gargadin cewa ba zata lamunci duk wani yunƙuri na ɓoye manufa don a sake shi ko kuma yi wa wasu malamai makamancin wannan tuhuma.

A ƙarshe, Kungiyar Ahlussunnah ta bukaci Gwamnatin Kano da ta fito fili ta bayyana matsayinta kan lamarin Abduljabbar domin kauce wa zargin boye gaskiya. Kungiyar ta yi kira ga shugabanni da su mutunta kotu, kare mutuncin addini, da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet