Connect with us

Featured

Rikicin Matatar Ɗangote Da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur Da Gas Na Iya Haifar Da Matsalar Katsewar Lantarki a Najeriya

Ƴan Najeriya na iya fuskantar barazanar shiga mawuyacin hali bayan ƙungiyar ma’aikatan manyan jami’an man fetur da iskar gas, PENGASSAN, ta fara yajin aiki a fadin ƙasar a yau Litinin 29 ga Satumba. Yajin aikin, wanda ya biyo bayan korar ma’aikata fiye da 800 a ma’aikatar man fetur ta Dangote, ya tilasta dakatar da isar da mai da iskar gas zuwa masana’antar. Lamarin da masana ke ganin zai iya jawo tashin farashin man fetur da kuma katsewar wutar lantarki, ganin cewa fiye da kashi 70% na wutar Najeriya na fitowa daga tashoshin iskar gas.

Shugabannin ƙungiyar sun ce za su ci gaba da yajin aikin har sai an mayar da ma’aikatan da aka kora, tare da zargin masana’antar Dangote da karya dokokin ƙwadago. Wannan mataki ya riga ya sa aka dakatar da aikin matatar man fetur da masana’antar takin zamani, yayin da ‘yan kasuwa suka gargadi cewa matsalar za ta jawo hauhawar farashi da koma bayan tattalin arziki. Kungiyar kamfanonin samar da wuta (GenCos) ta tabbatar da cewa, tuni aka umurce su da dakatar da aiki a tashoshin iskar gas, lamarin da zai iya jefa ƙasar cikin duhu baki ɗaya.

Kungiyoyi daban-daban sun yi kira ga gwamnati da ta shiga tsakani don dakatar da rikicin kafin ya ta’azzara. Kungiyar TUC ta bayyana goyon bayanta ga PENGASSAN, tana mai bayyana cewa ya zama wajibi a dawo da ma’aikatan da aka kora tare da neman afuwarsu. Sai dai masana’antar Dangote ta mayar da martani da cewa matakin PENGASSAN ya saba doka, kuma manufarsa ita ce cutar da ‘yan Najeriya. Ta ce korar ma’aikatan ta shafi batutuwan tsaro da ingancin aiki, ba wai danniya ga ‘yan ƙungiya ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet