Connect with us

Featured

Rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano Ta Kama Masu Laifi 105 a Wata Guda

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara a yaki da aikata laifuka, musamman ta hanyar shirin ta na musamman mai suna “Operation Kukan Kura”. Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Jihar, Bompai, Kano. Ya ce rundunar ta kara kaimi wajen dakile miyagun ayyuka da tabbatar da tsaro, musamman a wannan lokaci na karshen shekara da ake samun yawan zirga-zirgar mutane, kasuwanci da girbin amfanin gona.

A cewar Kwamishinan, shirin Operation Kukan Kura an tsara shi ne don magance dukkan nau’o’in laifuka tare da hadin kai da al’umma, amfani da basira da kuma fasahar zamani. Ya ce wannan tsari ya taimaka matuka wajen dakile ayyukan bata-gari tun kafin su faru da kuma bayar da martani cikin gaggawa ga barazanar tsaro. “Mun samu raguwar laifuka sosai, mun kuma kama masu aikata manyan laifuka tare da kwato makamai masu hadari da miyagun kwayoyi,” inji shi.

Ya bayyana cewa a cikin watan Satumba kadai an kama mutane 105 da laifuka 30, ciki har da fashi da makami, safarar miyagun kwayoyi, satar motocin hawa, adaidaita sahu da babura, da kuma yan daba. Rundunar ta kwato manyan makamai, motocin hawa, babura, shanu da miyagun kwayoyi. Kwamishinan ya ce an kwato kwayoyin Tramadol da Pregabalin da kudinsu ya kai N82,725,000 a Unguwar Rimin Auzinawa Kano, da kuma tabar Wiwi sinki 523, wanda za a mika wa NDLEA don ci gaba da bincike da gurfanarwa a gaban kotu.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa rundumar ta kuma kama kwayoyin Tramadol da kudinta ya kai Naira miliyan 60.3 da kwayar Pregabalin ta Naira miliyan 22.4 da kuma sinki 523 na tabar wiwi da injinan tura kudi na POS guda biyar daga hannun wadanda ake zargi a sassan jihar.

CP Bakori ya gode wa al’ummar Jihar Kano bisa goyon bayan da suke baiwa ‘yan sanda, yana mai tabbatar da cewa za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Ya kuma bukaci jama’a su ci gaba da bayar da hadin kai domin dorewar zaman lafiya. Kwamishinan ya jinjinawa manema labarai bisa kokarinsu na yada sahihan bayanai ga al’umma kan kokarin rundunar wajen yaki da laifuka a Jihar Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet