Featured
Gwamnatin Habasha Ta Haramta Shigar Da Manyan Motoci Masu Amfani Da Man Fetur Cikin Ƙasar

Firaministan ƙasar Ethiopia, Abiy Ahmed, ya sanar da cewa gwamnati ta haramta shigar da manyan motoci masu amfani da man fetur zuwa ƙasar. Abiy ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da matakin farko na masana’antar iskar gas ta LNG da aka gina a yankin Somali da ke gabashin ƙasar, kamar yadda gidan talabijin na gwamnati (ETV) ya ruwaito. Wannan mataki, in ji shi, na nufin sauya tsarin sufuri zuwa amfani da iskar gas domin rage dogaro da man fetur.
Firaministan ya bayyana cewa gwamnati za ta ba da damar shigo da manyan motoci masu amfani da iskar gas ba tare da biyan haraji ba. Wannan wani bangare ne na manufofin gwamnatin wajen karfafa amfani da makamashi mai tsafta, tare da sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa damar sauyawa daga man fetur zuwa iskar gas.
An bayyana cewa wannan matakin ya yi daidai da irin wanda aka ɗauka tun a watan Janairun 2024, lokacin da gwamnati ta fara haramta shigo da motoci masu amfani da man fetur. Ko da yake Firaministan bai fayyace dalilan wannan sabuwar doka kai tsaye ba, masana sun danganta ta da tsadar farashin man fetur a ƙasar da kuma manufofin gwamnati na yaƙi da sauyin yanayi.
Masana’antar LNG da aka kaddamar ana sa ran za ta samar da sama da lita miliyan 100 na iskar gas a kowace shekara a matakin farko. Haka kuma, Abiy Ahmed ya kaddamar da mataki na biyu na aikin, wanda ake sa ran idan an kammala shi, zai samar da kimanin lita biliyan 1.33 na iskar gas a duk shekara, matakin da zai ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar tare da rage dogaro da makamashin da ke gurbata muhalli.