Featured
NAFDAC Ta Lalata Gurɓatattun Magunguna na Naira Biliyan 15
Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta lalata gurbatattun magunguna da kayayyakin jabu, da waɗanda wa’adin aikin su ya ƙare da kimar su ta kai Naira biliyan 15 a Ibadan, Jihar Oyo. Darakta Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana hakan ne a lokacin da aka gudanar da taron kona kayan a ranar Alhamis 02 ga Oktoba, inda ta jaddada cewa hukumar na da cikakken tsari wajen tabbatar da tsabtar abinci da ingancin magunguna a Najeriya.
Adeyeye, wacce Daraktan Bincike da Aiwtar da Dokoki na NAFDAC, Martins Iluyomade, ya wakilta, ta bayyana cewa kayan da aka lalata sun haɗa da magungunan da aka haramta da waɗanda ba su da rajista kamar su Analgin, Cocodamol, codeine cough syrup, tramadol, oxytocin, da wasu rigakafi daban-daban. Ta ce lalata kayayyakin zai hana su sake shiga kasuwa, tare da kare lafiyar ‘yan ƙasa daga haɗarin magungunan da ba su dace ba.
Ta gode wa hukumomin tsaro irin su ‘yan sanda, sojoji, DSS, NDLEA, NSCDC, da Majalisar Magunguna ta Ƙasa bisa haɗin kan da suke bayarwa wajen yaƙi da magungunan jabu. Haka kuma ta ja hankalin iyaye da al’umma su guji siyan magunguna daga masu sayarwa ba bisa ƙa’ida ba tare da wayar da kan matasa kan haɗarin hakan.
Shi ma wakilin shugaban Hukumar Kwastam, S.K. Tijani, ya ce akwai haɗin gwiwa tsakanin NAFDAC da Kwastam wajen hana shigo da magunguna da kayayyakin da ba su dace ba, inda ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki su taka rawar gani wajen tabbatar da Najeriya ta tsabtace daga irin waɗannan laifuffuka.
