Addini
Ban Taɓa Yunƙurin Musuluntar Da Matata Ba – Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ’yan Najeriya ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba. Ya bayyana hakan ne a wajen jana’izar Nana Lydia Yilwatda, mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda aka gudanar a Cocin COCIN, Jos, Jihar Plateau. Tinubu ya bayyana cewa duk da shi Musulmi ne, matarsa Fasto ce, kuma bai taɓa ƙoƙarin sauya mata addini ba domin ya na girmama ’yancin kowane mutum. Ya yi kira ga jama’ar Plateau da su ƙaurace wa kiyayya da rarrabuwar kai, tare da yin aiki don ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Shugaban ƙasar ya kuma tabbatar wa shugabannin coci-coci na Arewa cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da adalci ga dukkan addinai tare da ɗaukar matakai na gaskiya wajen magance matsalar rashin tsaro. Ya ce gwamnatin tarayya na ƙoƙarin murƙushe ta’addanci, satar mutane da rikicin manoma da makiyaya a faɗin ƙasar. A yayin taron, Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya gode wa shugaban ƙasa bisa halartar jana’izar, tare da bayyana cewa matsalar tsaro ita ce babban kalubale ga cigaban jihar.
A cikin jawaban Farfesa Yilwatda, ya bayyana mahaifiyarsa a matsayin mace mai ƙwazo da juriya wadda ta rayu a kan magani tsawon shekaru 47 amma ta ci gaba da tallafawa iyali da al’umma. Ya gode wa shugaban ƙasa da sauran manyan baki da suka nuna masa goyon baya a lokacin rasuwar. Daga cikin waɗanda suka halarta akwai gwamnoni masu ci da wadanda su ka sauka, ministoci, ’yan majalisa, shugabannin addini da na gargajiya.
Sai dai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya soki ziyartar Tinubu zuwa Plateau domin halartar jana’izar, yana mai cewa hakan na nuna rashin fifita jin daɗin talakawa da mutanen da rikice-rikice suka shafa. Atiku ya ce da dama daga cikin jihohin Arewa ta Tsakiya sun fuskanci hare-hare masu muni, amma shugaban ƙasa bai taɓa kai ziyara don jajantawa waɗanda abin ya shafa ba. Ya bayyana tafiyar Tinubu Plateau domin halartar abin da ya kira “bikin siyasa” a matsayin rashin tausayi da nuna banbanci tsakanin shugabanni da jama’a.
