Addini
Gwamnatin Kano Ta Fara Shirye-shiryen Aurar Da Mutane 2,000 a Faɗin Jihar

Gwamnatin Jihar Kano ta ba da umarni ga Hukumar Hisba ta jihar da ta fara shirye-shiryen gudanar da auren mutane 2,000 karkashin shirin auren gata na gwamnati. Mataimakin Kwamanda Janar na hukumar, Sheikh Mujahid Aminudeen, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da jaridar PUNCH Online ta wayar tarho a ranar Alhamis 09 ga Oktoba, inda ya ce nan ba da jimawa ba za a fara aiwatar da dukkan shirye-shiryen domin tabbatar da nasarar wannan gagarumin bikin aure.
Sheikh Mujahid ya ce shirin na karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, kuma dukkan ma’aurata da ke son shiga auren dole ne su yi rajista kafin su cancanci shiga. Ya ƙara da cewa, akwai matakai na musamman da ake bi kafin gudanar da auren, ciki har da cikakken binciken lafiya wanda ya haɗa da gwajin cutar HIV/AIDS, Hepatitis, jini (genotype), da kuma gwajin amfani da miyagun ƙwayoyi. Duk wanda bai je wannan bincike ba, zai rasa damar shiga shirin.
A cewar hukumar, an dawo da shirin auren gatan ne domin tallafa wa mata musamman marasa galihu, marasa aure, zawarawa da kuma waɗanda iyayensu ba su da ikon ɗaukar nauyin shirya musu aure. Wannan mataki na gwamnatin Gwamna Yusuf na da nufin rage yawaitar karuwanci da wasu munanan dabi’u da ke faruwa a cikin al’umma, musamman a tsakanin zawarawa da ‘yan mata a jihar.
Shirin auren gatan ya kasance ɗaya daga cikin manyan tsare-tsaren jinƙai na gwamnatin jihar Kano a baya, kuma sake farfado da shi yana nuna niyyar gwamnati ta tallafa wa al’umma wajen inganta zamantakewa da rage matsalolin tattalin arziki da ke hana mutane damar yin aure cikin sauƙi.