Connect with us

Featured

Rahoton Bankin Duniya Kan Yadda Talauci Ya Ƙaru a Mulkin Tinubu Gaskiya Ne – ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya amince da rahoton Bankin Duniya na watan Oktoba 2025, wanda ya nuna cewa mutane miliyan 139 a Najeriya yanzu suna rayuwa cikin ƙangin talauci. Jam’iyyar ta ce wannan rahoto ya zama hujja mai ƙarfi da ke fallasa gazawar manufofin tattalin arziƙin gwamnatin APC mai mulki. ADC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa ta bakin mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, inda ta ce rahoton ya tona asirin bambanci tsakanin ikirarin cigaba na gwamnati da halin matsin rayuwa da al’umma ke ciki.

Rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa adadin talakawa ya tashi daga miliyan 81 a 2019 zuwa miliyan 139 a 2025 — abin da ke nuni da cewa kusan kashi 61% na al’ummar ƙasar na fama da matsanancin talauci. Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da wannan kididdiga, tana cewa ba ta da tushe kuma ba ta nuna ainihin halin tattalin arziƙin Najeriya ba. Sai dai ADC ta zargi gwamnati da yin amfani da bayanan bogi domin ɓoye gazawar tattalin arziƙinta.

ADC ta ce, “A 2019, mutum 4 cikin 10 ne suke cikin talauci, amma a yau, mutum 6 cikin 10 ne ke fama da talauci mai tsanani. Yayin da gwamnati ke ta shelar samun karin kudaden shiga da nasarorin tattalin arziƙi, farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi, inda farashin buhun shinkafa ya ninka fiye da sau biyar cikin shekaru huɗu”.

Jam’iyyar ta kara da cewa tsarin tallafin jin kai ya rushe, inda yawan wadanda ke cin gajiyar shi ya sauka daga kashi 20% a 2019 zuwa kashi 6% a 2025. ADC ta bukaci gwamnatin Tinubu ta daina dogaro da maganganu kawai, ta mai da hankali kan samar da abinci, ayyukan yi, da kariyar zamantakewa domin taimaka wa miliyoyin ‘yan Najeriya da ke fama da talauci. Jam’iyyar ta ce maimakon gwamnati ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya, ya kamata ta ɗauki matakan gyara cikin gaggawa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetjojobetcasibomcasibommatbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantgrandpashabetcasibomnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet