Connect with us

Featured

Yawancin Ƴan Fansho Dubu Biyar Su Ke Karɓa a Wata – NUP

Ƙungiyar Ƴan fansho ta Ƙasa (NUP) ta bayyana damuwarta kan halin ƙuncin da mambobinta ke ciki, musamman a matakin jihohi, inda ta ce har yanzu akwai masu ritaya da ke karɓar fanshon da bai wuce N5,000 a wata, duk da tsadar rayuwa da ke ƙaruwa. Sakataren Ƙungiyar, Actor Zal, ya ce jihohi da dama sun kasa ba da fifiko wajen kula da tsoffin ma’aikata, inda ya bayyana cewa jihohi 13 kacal ne ke biyan fansho da alawus akai-akai. Ya ce sabanin matakin jihohi, tsoffin ma’aikatan tarayya na cikin mafi kyawun matsayi saboda mafi ƙarancin fanshonsu na N32,000 a wata.

Zal ya bayyana cewa N5,000 a wannan zamani ba zai iya ciyar da mutum ba, musamman ganin yadda farashin kaya da rayuwa suka tashi. Ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da roƙon gwamnati ta ɗauki matakai na gaggawa domin kula da walwalar masu ritaya. Ya kuma yi suka kan tsarin rancen gwamnati ga masu ritaya, wanda aka kaddamar ta Cibiyar Lamunin Masu Amfani da Kayayyaki (CREDICORP) tare da Leadway Trustees da Optimus Bank. Tsarin ya ba da damar samun lamuni daga N50,000 zuwa matsakaicin adadi bisa ga yawan fanshon mutum.

Sai dai Zal ya bayyana cewa tsarin rancen ba zai magance matsalolin masu ritaya ba, illa ya ƙara musu nauyi. “Ina za su samo kuɗin mayar da rance daga wannan ɗan fanshon da ake basu? Wannan tamkar zuba ruwa a rariya ne. Wannan ba mafita ba ce, illa dai matsala ce,” in ji shi.

Ƙungiyar NUP ta sake jaddada bukatar ta na kafa mafi ƙarancin fansho na N60,000 domin rage tasirin hauhawar farashin kaya ga masu ritaya. Ta kuma nemi gwamnati ta samar da inshorar lafiya ta dole, rangwamen sufuri da tallafin abinci ga masu ritaya. Zal ya yi kira ga gwamnati ta sake duba tsarin fanshon haɗin gwiwa (contributory pension scheme), saboda yadda yawancin tsoffin ma’aikata ke fama da ƙarancin kudaden fansho. Ya ce dole ne a tabbatar da cewa duk wani ƙarin albashi ko fansho a nan gaba ya shafi tsoffin ma’aikata a dukkan tsare-tsaren fansho domin tabbatar da adalci da dorewa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet