Connect with us

Featured

Shugaba Tinubu Zai Tafi Ƙasar Italiya a Yau Lahadi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai tashi zuwa Italiya a yau Lahadi 12 ga Oktoba, domin halartar taron shugabannin ƙasashe kan tsaro da ake kira Aqaba Process Heads of State and Government Level Meeting. Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa taron zai mayar da hankali ne kan ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin Afirka ta Yamma.

Za a fara gudanar da taron ne a ranar 14 ga watan Oktoba, inda shugabanni da manyan jami’an tsaro daga ƙasashen Afirka za su haɗu domin tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin. Sarkin Jordan, Abdullah II, ne ya ƙaddamar da taron Aqaba a shekarar 2015 domin haɗa kai wajen yaƙar ta’addanci. Masarautar Jordan da gwamnatin Italiya ne ke gudanar da taron a bana.

A cewar fadar shugaban ƙasa, Tinubu zai yi amfani da wannan dama wajen ganawa da wasu shugabannin ƙasashe a bayan taron domin lalubo sabbin hanyoyi na haɗin gwiwa wajen magance matsalolin tsaro a nahiyar. Taron na zuwa a lokacin da yankin Afirka ta Yamma ke fuskantar ƙalubale daga ‘yan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya.

A cikin tawagar shugaban akwai Ministan Tsaro, Badaru Abubakar; Ƙaramar Ministar Harkokin Waje, Bianca Ojukwu; Mai Ba da Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu; da Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri (NIA), Mohammed Mohammed. Za su kasance tare da shugaban domin halartar taron da kuma tattaunawa da sauran shugabanni.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet