Connect with us

Featured

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Jita-jitar Sauke Ministan Kuɗi Wale Edun

Fadar Shugaban Ƙasa ta karyata jita-jitar cewa Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun, yana fama da hawan jini, ko kuma zancen da ake yaɗawa cewa an fita da shi ƙasar waje don jinya. Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar cewa Edun yana gida a Abuja yana murmurewa daga rashin lafiya, kuma shugaba Tinubu bashida wani shiri na sauke shi daga muƙaminsa.

Wani babban jami’i ya bayyana cewa lallai Edun na fama da rashin lafiya mai ɗan tsanani, amma ba hawan jini ba ne kamar yadda ake yadawa. Ya ce likitocin Najeriya ne ke kula da shi a yanzu, kuma idan akwai bukatar neman ƙarin kulawa a waje, za a yi hakan. Hakazalika, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya tabbatar cewa Edun yana Najeriya kuma yana samun sauƙi.

Rahotanni sun bayyana cewa ba zai halarci taron shekara-shekara na Bankin Duniya da IMF ba, wanda za a gudanar a Washington DC daga 14 ga Oktoba. Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, zai jagoranci tawagar Najeriya a madadinsa. Wannan ya haifar da jita-jita cewa shugaban ƙasa na shirin sauya shi, wanda fadar gwamnati ta musanta.

Edun, wanda aka nada a watan Agusta 2023, na daga cikin manyan ministocin da ke jagorantar sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, ciki har da daidaita darajar Naira, rage hauhawar farashi, da jawo hannun jarin daga waje. Ya taba zama kwamishinan kuɗi a Jihar Legas tsakanin 1999 da 2004. Sai dai har yanzu ma’aikatar kuɗi ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan halin da yake ciki ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet