Featured
Gwamnatin Kano Za Ta Samar Da Kamfanin Ƙera Kayan Sola
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a kafa masana’antun ƙera fanel da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki ta hasken rana a jihar. Wannan ci gaban ya biyo bayan rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin gwamnati da kamfanonin Tricell Solar Solutions da IRS Green Energy
An cimma wannan yarjejeniya ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA), a yayin taron Sabunta Makamashi na Najeriya (NERIF) na 2025 da aka gudanar a Abuja. Shugaban hukumar zuba jari ta jihar (Kan-Invest), Naziru Halliru, ya jagoranci ƙulla yarjejeniyar a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin Kano ta ce wannan mataki na daga cikin shirye-shiryenta na faɗaɗa samar da makamashi mai tsafta da araha, da kuma bunƙasa masana’antu a cikin gida. Haka kuma, ana sa ran hakan zai taimaka wajen ƙirƙirar dubban guraben aikin yi ga matasa a fadin jihar.
A karkashin tsarin, kamfanin IRS Green Energy zai gina masana’antar da za ta rika samar da kayan hasken rana da ƙarfin 600MW a shekara, yayin da Tricell Solar Solutions zai kafa wata masana’anta mai ƙarfin 500MW. Wannan zai mayar da Kano cibiyar samar da makamashi mai sabuntawa a Arewacin Najeriya.
