Featured
Kano: Kotu Ta Yankewa Mai Horar Da Ƴan Wasan Kwallon Ƙafa Hukuncin Shekaru 8 a Gidan Gyaran Hali

Kotun Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahuru Muhammad ta yanke wa wani mai horar da ƴan wasan ƙwallon ƙafa, Hayatu Muhammad, hukuncin zaman gidan yari na shekaru takwas ba tare da zabin biyan tara ba. An kama shi da laifin yin lalata da ɗan wasansa har sau biyu a wurare daban-daban a Dala, Kano.
Mai gabatar da ƙara, Ibrahim Arif Garba, ya kira shaidu guda biyar domin tabbatar da laifin. Duk da cewa wanda ake tuhuma ya fara musanta zargin, shaidu sun tabbatar da aikata laifin. A karshe, shi kadai ne ya tsaya shaida a wajen kare kansa.
Mai shari’a Dahuru ya tabbatar da cewa an samu kocin da laifi bisa hujjojin da aka gabatar. Ya yanke masa hukuncin shekaru huɗu-huɗu kan kowane laifi biyu da ya aikata.
Sai dai kotu ta umarci cewa hukuncin ya gudana a lokaci guda, wanda hakan ya sa jimillar zaman gidan yari ya tsaya a kan shekaru takwas kacal.