Connect with us

Featured

Nnamdi Kanu Yana Da Cikakkiyar Lafiyar Da Zai Iya Fuskantar Shari’a – NMA

Kungiyar Likitocin Nijeriya (NMA) ta bayyana wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, yana da cikakkiyar lafiyar da zai iya fuskantar Shari’a a halin yanzu. Kwamitin likitocin da shugaban NMA ya kafa ne ya gudanar da cikakken binciken lafiyarsa bisa umarnin kotu, bayan samun sabanin rahotanni daga lauyoyin gwamnati da na Kanu.

 

A cewar rahoton da aka mika wa kotu a ranar 13 ga Oktoba, likitocin sun tabbatar cewa cutar da ke damun Kanu ba ta da wani hatsari, kuma hakan ya tabbatar masa da dacewar ci gaba da shari’a. Bisa wannan hujja, alkalin kotun, Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana gamsuwarsa tare da bada umarnin cigaba da shari’ar ba tare da wata tangarda ba.

 

Kotun ta tanadi kwanaki shida a jere daga 23 ga Oktoba domin Kanu ya fara kare kansa tare da kammala shaidarsa. Wannan mataki na zuwa ne bayan jinkiri da dama da aka samu a shari’ar saboda batun lafiyar sa.

 

Haka kuma, kotun ta amince da roƙon lauyan Kanu, Chief Kanu Agabi (SAN), na samun damar tattaunawa ta sirri da wanda yake karewa ba tare da tsangwama daga hukumar DSS ba. An tsara ganawar sirrin a ranar 22 ga Oktoba a cikin harabar kotu tsakanin ƙarfe 9:00 na safe zuwa 12:00 na rana.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet