Featured
Jihohin Kano, Katsina da Jigawa Sun Yi Haɗin Gwiwa Don Bunƙasa Wutar Lantarki a Yankunansu

Gwamnatocin jihohin Kano, Katsina da Jigawa sun rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya ta haɗin gwiwa domin bunƙasa kasuwar wutar lantarki a yankin Arewa maso Yamma. Wannan ya haɗa da zuba jari a kamfanin Future Energies Africa (FEA), babban mai zuba jari a Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO). Yarjejeniyar ta samo asali ne daga wani taro kan bunƙasa lantarki da aka gudanar a birnin Marrakech, Morocco, daga ranar 16 zuwa 19 ga Oktoba, 2025.
A cewar Kwamishinan Wutar Lantarki da Makamashi na Kano, Dr. Gaddafi Sani Shehu, jihohin uku za su yi aiki kafada da kafada wajen gano sabbin hanyoyi da za su inganta kasuwannin wutar lantarki, tare da kafa tsare-tsaren doka da tsarin haɗin gwiwa mai dorewa. Ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen karfafa dabarun KEDCO da haɓaka rarraba wutar lantarki ga dubban al’ummomi a yankin.
Kwamishinan ya ce an tsara kashe naira biliyan 50 don aiwatar da shirin, wanda ya haɗa da samar da wuta ta hanyar tsarin hasken rana da na cikin gida. Haka kuma, za a yi aiki tare da KEDCO domin rage asarar wutar lantarki daga masu amfani, matakin da zai tabbatar da samar da wuta mai inganci da dorewa ga jama’a.
Bugu da ƙari, jihohin sun amince da gudanar da taron kasa da kasa duk shekara, tare da ganawa sau huɗu a kowace shekara domin bibiyar ci gaban ayyuka, tsara sabbin manufofi da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa a kasuwar wutar lantarki. Wannan hadin gwiwar ana sa ran zai kawo sauyi mai ma’ana a fannin samar da wutar lantarki a Arewa maso Yamma.