Featured
Kwastam Ta Kama Ƙwayoyin Kimanin Naira Biliyan 5.3 a Lagos
Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Tin Can Island da ke Legas, ta kama kwayoyi da miyagun abubuwa da kudinsu ya kai naira biliyan 5.3, bayan an gano an boye su a cikin motocin da aka shigo da su daga ƙasashen waje. Kwamptrola Frank Onyeka, wanda ke jagorantar hukumar a tashar, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, yana mai cewa an samu nasarar ne ta hanyar amfani da bayanan sirri da bincike mai zurfi.
Kwamptrola Onyeka ya bayyana cewa kwantena ta farko, mai lamba HLXU8500072, daga Montreal, Canada, an cafke ta tun ranar 4 ga Satumba, inda aka gano 156 fakiti na Colorado Indica da nauyinsu ya kai kilo 78, da kuma Hashish Oil kilo 1.2, duk an ɓoye su a cikin motoci huɗu. Sai kuma wani kwantena mai lamba FANU312876/9 da aka kama ranar 24 ga Oktoba, wanda ke ɗauke da 2,081 fakiti na Cannabis Indica da Crystal Methamphetamine kilo 8.
Onyeka ya ce an mika dukkan kayan ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin ci gaba da bincike da gurfanarwa a kotu. Ya yaba da haɗin gwiwar jami’an NDLEA, Rundunar Sojan Ruwa, da ‘yan sanda wajen gudanar da aikin, tare da jaddada cewa Kwastam za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare iyakokin ƙasa da tabbatar da bin ƙa’idojin cinikayya.
A nasa bangare, kwamandan NDLEA a Tin Can, Daniel Onyishi, ya gode wa hukumar Kwastam bisa himma da jajircewarta, yana mai cewa hadin kai tsakanin hukumomin tsaro ya taka rawar gani wajen dakile safarar miyagun kwayoyi. Ya tabbatar da cewa za su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da hukunci bisa doka.
