Connect with us

Featured

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Ragu a Lokacin Tinubu – NOA

Hukumar Kula da Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) ta bayyana cewa basussukan Najeriya sun ragu sosai tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023. Hukumar ta ce duk da cewa wasu rahotanni na ƙarya na yawo kan yadda bashin ƙasar ke ƙaruwa, ainihin bayanai daga Hukumar Kula da Bashin Ƙasa (DMO), Babban Bankin Ƙasa (CBN), da Ma’aikatar Kuɗi sun nuna raguwar bashin daga dala biliyan 113.42 a watan Yunin 2023 zuwa dala biliyan 94.22 a ƙarshen shekarar 2024.

NOA ta bayyana cewa wannan raguwar ta fi dala biliyan 19 a cikin watanni 18, alamar cewa gwamnatin Tinubu tana biyan wasu daga cikin tsoffin basussuka maimakon ƙara aro sabbi. Hukumar ta ce wannan ya nuna ana tafiyar da kuɗin ƙasa cikin kwarewa, inda bashin da ake biya daga kuɗaɗen shiga ya ragu daga kashi 97 cikin 100 a farkon 2023 zuwa ƙasa da kashi 50 cikin 100 a tsakiyar 2025.

A cewar NOA, gwamnatin ta kuma biya bashin IMF na dala biliyan 3.26 a cikin shekaru biyu, tare da kashe kusan dala biliyan 7 wajen biyan bashin ƙetare a farkon watanni 18 na mulkin Tinubu. Haka kuma an samu ci gaba wajen tara kuɗaɗen haraji da na kwastam, inda harajin FIRS ya ƙaru da kashi 30, yayin da Hukumar Kwastam ta tara Naira tiriliyan 1.3 a watanni hudun farko na 2025 — fiye da ninki biyu idan aka kwatanta da shekarar 2023.

Hukumar ta ƙara da cewa tattalin arzikin Najeriya yana nuna alamun farfaɗowa, musamman a fannin noma, fasaha, da sabis. Ta ambaci hasashen Bankin Duniya da ke cewa tattalin arzikin ƙasar zai bunƙasa da kashi 3.7 cikin 100 a shekarar 2024 — mafi girma cikin shekaru kusan goma, baya ga lokacin bayan annobar korona. NOA ta jaddada cewa gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin rage dogaro da man fetur ta hanyar ƙarfafa masana’antu da saka hannun jari a ƙananan sana’o’i da ayyukan dijital.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet