Featured
Tinubu Zai Gana da Trump Kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya – Bwala

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, za su gana a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa domin tattauna batun zargin kisan kiyashi na Kiristoci a Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan Trump ya zargi gwamnatin Najeriya da “yin shiru” kan hare-haren da ake kaiwa Kiristoci, inda ma ya yi barazanar kai farmaki da kuma katse tallafi ga ƙasar.
Bwala ya bayyana a shafinsa na X cewa wannan ganawa za ta mai da hankali kan yaki da ta’addanci da ‘yan tada kayar baya, wanda ya ce Tinubu da Trump na da ra’ayi ɗaya a kai. Ya kuma tunatar da cewa Trump ne ya ba da izinin sayar wa Najeriya makamai tun da farko, abin da gwamnatin Tinubu ta yi amfani da shi wajen samun nasarori a yaƙin da ake da ta’addanci.
Ya ce duk wata rashin fahimta da ke tattare da batun ko ‘yan ta’addan na kai hari ne ga Kiristoci kaɗai ko kuma dukkan addinai, za ta kasance cikin abubuwan da shugabannin biyu za su tattauna don samun fahimtar juna da mafita mai dorewa.
A cewar Bwala, za a iya gudanar da ganawar ne ko dai a Fadar Shugaban Ƙasa ta Abuja ko kuma a Fadar White House a Washington, bisa jadawalin da ake kammalawa. Ya kara da cewa tattaunawar za ta zama wata dama ta ƙarfafa dangantakar Amurka da Najeriya, tare da tabbatar da cewa yaƙi da ta’addanci yana da goyon bayan ƙasashen duniya.