Featured
A Karon Farko Musulmi Ya Lashe Zaɓen Magajin Garin New York

Zohran Mamdani, ɗan jam’iyyar Democrat, ya lashe zaɓen magajin garin birnin New York, lamarin da ya kafa tarihi a matsayin musulmi na farko da ya taɓa rike wannan kujera. Mamdani, wanda shi ma shi ne mafi ƙarancin shekaru cikin masu rike wannan matsayi, ɗan asalin Asiya ne wanda ya taso a Amurka.
A wannan zaɓen, Mamdani ya doke Andrew Cuomo na jam’iyyar Indifenda da Curtis Sliwa na jam’iyyar Republican, wanda ake ganin shi ne zai kasance na uku. Nasararsa ta zo a rana ɗaya da ake ganin jam’iyyar Democrat ta yi rawar gani a wasu muhimman wurare a faɗin Amurka.
Masu sharhi suna kallon wannan zaɓe a matsayin wata alamar canji da ke rage tasirin gwamnatin shugaban kasa Donald Trump a siyasar ƙasar. Wasu kuma na ganin yana iya zama sabon babi ga siyasar biranen manyan jihohi a nan gaba.
Duk da haka, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa wannan zaɓen ba ya shafarsa kai tsaye, yana mai cewa shi ba ya cikin masu takara, don haka sakamakon bai zame masa wani ƙalubale kai tsaye ba.