Featured
Ba Zan Yi Sharhi Kan Gwamnatin Tinubu a Yanzu Ba — Wole Soyinka

Fitaccen marubuci kuma mai lambar yabo ta Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ce ba zai fara yin cikakken sharhi kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiya ba a halin yanzu. Soyinka ya bayyana cewa a duk lokacin da ya yi tsokaci kan al’amuran mulki, ana karkatar da maganganunsa, don haka zai ɗauki lokaci kafin ya fitar da ra’ayinsa a rubuce.
A wani hira da BBC News Yoruba, Soyinka ya ce mutane da dama suna tambayarsa ra’ayinsa kan gwamnatin Tinubu, amma ya zaɓi yin shiru saboda yawan canza masa kalamansa da ake yi. Ya ce da zarar ya ga lokaci ya yi, zai yi cikakken bayani game da fahimtarsa kan halin da ƙasar take ciki.
Soyinka, wanda yayi suka kan gwamnatocin baya ciki har da gwamnatin Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, har yanzu bai yi tsokaci kan gwamnatin Tinubu ab, duk da sama da shekaru biyu da ta shafe tana mulki. A baya ya yi suka mai tsanani kan yadda gwamnatin Buhari ta yi mu’amala da matsalolin tsaro a ƙasar.
Haka kuma, Soyinka ya bayyana batun janye masa bizar Amurka, inda ya ce ba zai sake neman sabuwa ba ko zuwa yin wata takaddama da ofishin jakadancin Amurka. Ya ce idan Amurka ta yanke shawarar mayar masa da bizar, to su kawo masa gida, domin shi ba ya cikin rigima da jama’ar Amurka, sai dai da tsarin hukuma ne kawai.