Featured
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mata 5 a Shanono

‘Yan bindiga sun kai hari a kauyen Yan Kwada da ke karkashin yankin Faruruwa, karamar hukumar Shanono a Jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata biyar ciki har da masu shayarwa. Shaida daga yankin ta ce maharan sun iso ne da tarin yawa, dauke da makamai, suka shiga gidaje suna harbe-harbe da tsoratar da mutanen gari, kafin su tafi da wadanda suka kama.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin wadannan mata biyar, biyu sun samu damar komawa gida, yayin da sauran uku har yanzu suke hannun masu garkuwa. Wannan harin ya zo ne mako guda bayan rundunar hadin gwiwa ta sojoji ta yi artabu da ‘yan bindigar a yankin, inda aka kashe 19 daga cikinsu.
Mazauna Faruruwa da wasu kauyuka makusanta da ke kan iyakar Kano da Katsina sun dade suna fuskantar hare-hare masu maimaituwa, wanda hakan ya jefa su cikin fargaba da tashin hankali. Saboda tsanani da yawaitar hare-haren, wasu kauyuka sun watse, jama’a suna kaura zuwa Faruruwa ko kuma garuruwa na cikin birane don neman tsira.
A gefe guda, al’umma da shugabannin yankin na ci gaba da rokon gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara daukar matakin gaggawa, domin magance wannan matsala da ta jima tana addabar rayuwar jama’a da tattalin arzikin kauyukan yankin.