Connect with us

Featured

Tinubu Ya Yabawa Super Eagles Duk Da Rashin Samun Gurbin Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Super Eagles duk da ficewarsu daga neman gurbin zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, bayan da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta doke su a bugun fenariti a wasan zagaye na ƙarshe na neman gurbi da aka yi a Morocco ranar Lahadi. Ya ce ko da yake rashin nasarar ta yi zafi, ya kamata a yabawa ‘yan wasan bisa ƙoƙarin da suka nuna tun daga wasan farko da suka yi.

Shugaban ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a gyara kura-kurai, tare da komawa teburin tattaunawa domin gano matsalolin da suka hana tawagar ta samu nasara. Ya ce dole hukumar ƙwallon ƙafa, ‘yan wasa, da sauran masu ruwa da tsaki su ɗauki darasi daga wannan koma baya domin inganta gaba.

Tinubu ya umarci Super Eagles da su mayar da hankali gaba ɗaya kan gasar African Cup of Nations (AFCON) da za a yi daga Disamba 2025 zuwa Janairu 2026 a Morocco. Ya ce dole ne tawagar ta yi duk mai yiwuwa don dawo da martabar ƙasar a fagen kwallon ƙafa.

A ƙarshe, Shugaban ya ƙarfafa gwiwar ‘yan wasan, yana mai cewa gwamnati da ‘yan Najeriya za su ci gaba da mara musu baya, domin ganin sun dawo da ɗaukakar Super Eagles a gasar Afirka mai zuwa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet