Connect with us

Featured

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Ɗaliban Makaranta a Neja

A Papiri, ƙaramar hukumar Agwara, jihar Niger, wasu ‘yan ta’adda sun kai mummunan farmaki a safiyar Juma’a, 21 ga Nuwamba 2025 tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na dare, inda suka sace ɗalibai da ma’aikatan Makarantar Katolika ta St. Mary’s. Har yanzu ba a tantance adadin waɗanda aka yi awon gaba da su ba, domin hukumomi na ci gaba da ƙididdiga.

Wata majiyar cocin Katolika ta tabbatar da afkuwar lamarin, tana mai cewa Ba za ta iya fayyace cikakkun bayanai ba har sai an fitar da sanarwar hukuma daga cocin. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce za su fitar da bayani daga baya, yayin da Ahmed Abdullahi Rofia, shugaban sashen rigakafi da agaji na karamar hukumar Agwara, ya tabbatar da hare-haren ta wayar tarho.

A cikin wannan rahoton, Kakaki24 ta tattara cewa wannan hari ya biyo bayan na baya-bayannan da ya faru a Maga, jihar Kebbi, inda aka yi garkuwa da dalibai 25, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a game da illar tabarbarewar tsaro a makarantun yankin Arewa. Haka kuma, tun ranar Alhamis ne aka rufe sama da makarantu 50 a jihar Kwara saboda barazanar ‘yan bindiga.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya soke tafiye-tafiye zuwa Afirka ta Kudu da Angola domin jagorantar matakan gaggawa kan tsaro. Wannan karo na sabbin hare-hare na sake nuni da yadda rashin tsaro ke ci gaba da barazana ga ilimi da lafiyar al’umma a Najeriya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet