Featured
Gwamnatin Tarayya Da Jihohin Katsina Da Filato Sun Rufe Makarantu Sakamakon Taɓarɓarewar Tsaro
A ranar Juma’a, 22 ga Nuwamba 2025, fargaba ta ƙaru a zukatan ƴan Najeriya, yayin da ‘yan bindiga suka kai mummunan hari a makarantar St Mary’s da ke ƙaramar hukumar Agwara, Jihar Neja, inda suka yi garkuwa da ɗalibai 215 da malamai 12. Kafin daga bisani a fitarvda sabon alkaluma dake nuna adadin ya kain303. Wannan farmaki ya faru ne kwana huɗu bayan sace ɗalibai mata 26 a Kebbi, wanda hakan ya sa Gwamnatin Tarayya da jihohi da dama su rufe makarantu, ciki har da rufe makarantu 41 na unity schools a faɗin ƙasa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa harin ya faru ne da ƙarfe 2 na dare, inda maharan da suka zo a kan babura sama da 100 suka ɗauki ɗaliban bayan ɗan lokaci da suka yi suna harbe-harbe. Shugaban CAN na Jihar Neja, Bulus Yohanna, ya tabbatar da adadin mutanen da aka sace, yayin da ‘yan sanda da sojoji suka tura jami’ai domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su. A baya-bayan nan, jihohin Kwara, Katsina, Plateau, Neja da Benue suma sun rufe makarantu saboda tsaro. Wannan lamari ya sake tayar da jijiyar wuya kan matsalar tsaro da makarantun yankin Arewa ke fuskanta.
Gwamnatin Neja ta ce St Mary’s ta karya umarnin da ya haramta buɗe makarantu a yankin saboda barazanar hare-hare, yayin da Gwamnatin Kebbi ta zargi jami’an soji da janye tsaro daga makarantar kafin hare-haren Kebbi kwana huɗu da suka gabata. Haka kuma, Gwamnonin Arewa sun yi kira da a ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare makarantun yankin, tare da jaddada cewa hare-haren na barazana ga yunkurin dawo da yaran da ba sa zuwa makaranta.
Iyalan waɗanda aka sace suna cikin tashin hankali, musamman mazauna Kebbi da suka yi kwanaki suna addu’a domin dawo da ‘ya’yansu. A gefe guda kuma, limaman cocin Katolika da shugabannin addinai sun bukaci gwamnati ta nuna ƙarfi wajen magance yawaitar hare-haren da suka ce “ba wai neman kuɗi ba ne, harin neman jini ne.” A halin yanzu hukumomi sun fara aikin ceto, yayin da ake sa ran gwamnati za ta ƙara tsaurara tsaro a makarantu a fadin Arewa.
