Featured
Gwamnatin Yobe Ta Sanar Da Rufe Makarantun Kwana a Jihar

A ranar Lahadi, 23 ga Nuwamba 2025, gwamnatin jihar Yobe ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun sakandiren kwana a fadin jihar sakamakon ƙaruwa da barazanar tsaro. Wannan matakin ya biyo bayan tashin hankali da aka samu a wasu jihohin arewacin ƙasar inda ’yan bindiga suka kai hare-hare kan makarantu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamna, Mamman Mohammed, ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa an yanke shawarar ne domin kare rayuka da dukiyoyin ɗalibai da malamai. Sanarwar ta ce gwamnatin ba za ta yi watsi da duk wata alamar barazana ga rayukan ɗalibai ba, musamman a makarantun kwana da ke da haɗarin fuskantar hare-hare.
A cewar sanarwar, matakin ya fito ne daga tattaunawar tsaro ta musamman da Gwamna Mai Mala Buni ya jagoranta, wadda ta mayar da hankali kan tsaron makarantu a fadin jihar. Kakaki24 ta tattaro cewa rufe makarantun zai fara aiki nan take har sai an tabbatar yanayin tsaro ya inganta, kuma hukumomi na ci gaba da duba yiwuwar sake buɗe su a mataki-mataki.
A makonni biyun da suka gabata, hare-haren da aka kai Neja, Kebbi, Filato da Katsina sun janyo tashin hankali tare da tilastawa gwamnatocin jihohin su rufe makarantunsu. Masu lura da al’amura na ganin cewa matakin Yobe wani ɓangare ne na ƙoƙarin kare ɗalibai daga fadawa cikin haɗarin da ke ci gaba da barazana ga ilimi a arewacin ƙasar.