Featured
Atiku Ya Koma Jam’iyyar ADC a Hukumance

24 ga Nuwamba 2025, — 12:30 p.m.
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a mazaɓarsa ta Jada da ke Jihar Adamawa, lamarin da ya kawo ƙarshen dogon jiran da ake yi game da inda zai nufa bayan ficewarsa daga PDP.
Atiku ya tabbatar da sauyin sheƙar ne ta shafinsa na X, inda ya wallafa hotunansa riƙe da katin sabuwar jam’iyyar tare da gajeren rubutu da ke nuna cewa ya shiga ADC a hukumance. Wannan na zuwa kusan watanni huɗu bayan fitar tasa daga PDP a cikin sanarwar da ya fitar ranar 14 ga Yuli, 2025.
A cewar rahoton Kakaki24, Atiku ya sha bayyana cewa ba zai iya ci gaba da zama a PDP ba saboda, a cewarsa, jam’iyyar ta kauce daga ainihin manufarta ta farko. Ya ce lokaci ya yi da zai ɗauki sabon mataki domin ci gaba da fafutukar siyasar da ya sa gaba.
Atiku Abubakar ya ce shiga ADC ɗin nasa wajibi ne bisa ga yanayin halin da PDP ta tsinci kanta, yana mai jaddada cewa siyasa tana buƙatar tsayawa kan gaskiya da bin muradun al’umma. Ya ce yana fatan sabuwar tafiyar za ta ba shi dama ya ci gaba da bada gudunmawa ga dimokuraɗiyyar Najeriya.