Featured
Fitaccen Jarumin Bollywood Dharamendra Ya Rasu

Fitaccen jarumin Bollywood, Dharmendra Kewal Krishan Deol, ya rasu yana da shekara 89 a ranar Litinin, 24 ga Nuwamba 2025, yayin da yake jinya a wani asibiti a birnin Mumbai, India. Mutuwar tasa ta tayar da hankalin masoya fina-finan Indiya a sassa daban-daban na duniya.
Shugaban gwamnatin India, Narendra Modi, ya yi jaje kan rasuwar, yana cewa Dharmendra “ya kawo ƙarshen wani gagarumin zamani a masana’antar Bollywood”. An haifi jarumin ne a Nasrali, gundumar Ludhiana, jihar Punjab, a ranar 8 ga Disamba 1935. Sunansa na farko shi ne Dharam Singh Deol, wanda mahaifinsa malami ya saka masa.
Dharmendra ya kasance jarumi mai matuƙar farin jini daga jama’a, musamman saboda rawar da ya taka a fina-finai sama da 300. Fitaccen salon aikinsa ya kai shi matsayin “He-Man na Bollywood”, yayin da rawar Veeru da ya yi a fim ɗin Sholay na 1975 ta zame masa alamar da ta fi daukar hankalin duniya.
Dharmendra ya rasu ya bar mata biyu — Prakash Kaur da Hema Malini — tare da ’ya’ya shida da jikoki goma sha uku. Masana’antar Bollywood da masoyansa a duniya suna ci gaba da tuna jarumin da ya yi fice wajen nishaɗantar da jama’a tsawon shekaru.