Featured
Mun San Maɓoyar Ƴanbindiga Amma Ba Za Mu Iya Yi Musu Luguden Wuta Ba – Gwamnatin Tarayya
Mai Ba wa Shugaba Tinubu Shawara kan Bayanai da Tsara Manufa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun san matsugunnai da ainihin ƙungiyoyin ’yan bindigar da ke da alhakin sace dalibai da fararen hula, ciki har da harin makon jiya a Makarantar Katolika ta St. Mary’s da ke Papiri, Jihar Neja. Ya ce duk da kasancewar akwai ingantattun bayanan sirri, amma harkar tsaro na fuskantar ƙalubale wajen kai farmaki kai tsaye saboda gudun jefa rayukan fararen hula cikin haɗari. Onanuga ya ce ko a baya anyi kuskuren luguden wuta a Borno, lamarin da ya sanya dakarun tsaro ke taka-tsantsan sosai.
A cewarsa, rashin cikakken jerin waɗanda aka sace na daga cikin abubuwan da ke sa gwamnati cikin duhu kan adadin mutanen da ake nema. Ya zargi hukumomin kananan yankuna da rashin bada hadin kai yadda ya kamata wajen tabbatar da bayanai, yana mai tambaya ko akwai wani ɓoyayyen manufa a cikin lamarin. Ya kuma ce dalilin da ya sa ba a shiga sansanonin ’yan bindiga nan take shi ne yadda masu garkuwa ke amfani da waɗanda suka sace a matsayin garkuwa don gujewa a kaddamar da farmaki.
A jawaban nasa, Onanuga ya yi karin haske kan umarnin Shugaba Tinubu na mayar da dubban jami’an tsaro daga hidimar VIP zuwa yankunan da ake fama da hare-hare, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa tsaro a muhimman wurare. Kakaki24 ta rawaito cewa Onanuga ya jaddada cewa gwamnatin ba ta musun cewa ana kashe ’yan Najeriya, amma tana ɗaukar matakai wajen dakile rikicin, kuma Shugaban Ƙasa zai yi jawabi ga al’umma bayan kammala shawarwari da hukumomin tsaro.
Ya kuma yi gargadi ga ’yan bindiga cewa rashin sakin wadanda suka sace zai haifar da farmaki mai ƙarfi daga gwamnati, yana mai cewa sun san illolin ƙi sakin waɗanda ke hannunsu. Onanuga ya nanata cewa gwamnati tana da cikakkiyar manufa ta sauya dabaru domin kare rayuka tare da kaucewa abin da zai iya janyo mummunan hasara ga fararen hula.
