Featured
2027 : Zan Kawo Ƙarshen Maguɗin Zaɓe a Najeriya – Shugaban INEC
A ranar Talata, 26 ga Nuwamba 2025, sabon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya sha alwashin kawar da magudi da sayen kuri’u a zaben 2027, yana mai cewa amincewar da ’yan Najeriya suka dora wa hukumar “amana ce mai tsarki” da ba za a yi wasa da ita ba. Amupitan ya yi wannan bayani ne yayin rantsar da Farfesa Adeniran Tella a matsayin sabon Kwamishinan Zabe na reshen Jihar Oyo a hedikwatar INEC da ke Abuja.
Amupitan ya bayyana nauyin da ke kan INEC a matsayin “muhimmin iki” yana mai jaddada cewa amincin tsarin zabe shi ne ginshikin dimokuradiyyar Najeriya. Ya gargadi Tella da cewa ba za a yarda da wani abu da zai tauye ka’idoji, tsari ko gaskiyar gudanar da zabe ba, tare da bukatar tabbatar da cewa ‘yan kasa sun samu kwarin gwiwa cewa kuri’unsu na da tasiri. Ya kara da cewa hukumar za ta dage wajen bin doka da aiwatar da dukkan matakai ba tare da kaucewa hanya ba.
A bangaren sa, Tella ya gode wa shugaban hukumar kan jagoranci da shawarwarin da ya bayar, tare da yin alkawarin aiki da hangen nesa da manufar INEC. Kakaki24 ta rawaito cewa Tella farfesa ne na tsare-tsaren gudanarwa da manufofin gwamnati, kuma ya taba kasancewa kwamishinan zabe a jihohin Oyo da Ekiti a baya, inda wa’adinsa na farko ya kare a watan Satumbar 2025.
