Featured
Rundunar Ƴansanda Ta Haramta Goyon Babur a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sake jaddada cikakken aiwatar da dokar da ta haramta ɗaukar fasinja da babura, tare da takaita zirga-zirgar adaidita sahu daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe. Wannan mataki na zuwa ne bayan gwamnatin jiha ta tabbatar da cewa dokar tana nan daram a kananan hukumomi tara da abin ya shafa, ciki har da Kano Municipal, Gwale, Dala, Fagge, Nassarawa, Tarauni, Kumbotso, Ungogo (Jido), da Dawakin Kudu (Tamburawa, Gurjiya da Jido).
Rundunar ’yan sandan ta ce an yi tanadin ƙungiyar musamman da za ta kama duk wanda ya karya doka, tare da tantance masu ƙoƙarin watsa bayanan da ba su da tushe. Jami’an tsaro sun bayyana cewa matakin na nufin ƙara tsaro da tabbatar da zaman lafiya ga al’umma, musamman ganin yadda wasu tattake dokar ke jawo rashin tsaro a daren Kano.
Kamar yadda Kakaki24 ta tattara, Kwamishinan ’Yan Sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga jama’a da su ba da haɗin kai wajen ganin doka ta yi aiki yadda ya kamata. Ya kuma roƙi al’umma su rika sanar da jami’ai duk wani abin da suka gani na karya doka ko abin da ke da zargin tada hankalin jama’a ta hanyar kiran layukan gaggawa na rundunar.
Rundunar ’yan sandan ta kara tabbatar da cewa KAROTA na cikin haɗin gwiwar aiwatar da wannan aiki, domin tabbatar da tsaro da kuma sauƙaƙa bin doka a fadin jihar. CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, ya tabbatar da cewa duk wanda aka samu da karya wannan doka zai fuskanci shari’a ba tare da wani jinkiri ba.