Featured
Yara 500,000 Da Basa Zuwa Makaranta Zasu Ci Gajiyar Tallafin Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabon shiri domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma inganta karatun manya a fadin ƙasar nan. Shirin, wanda Hukumar NMEC ta jagoranta, ya mayar da hankali wajen amfani da na’urorin zamani domin tattara bayanai da gano masu bukatar wannan taimako. An fara horar da masu tattara bayanan ne a Abuja domin tabbatar da ingantaccen aiki daga matakin farko.
Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 500,000 ne ake shirin ɗauka a zagaye na farko, musamman matasa masu shekaru 15 da suka daina karatu ko kuma wadanda ba su samu damar ci gaba ba. Shirin zai ba su damar koyo, sannan a tura su zuwa cibiyoyin koyon sana’o’i domin samun fasaha bayan kammala karatun. Dr. John Onimisi, ya ce aikin ya shafi dukkan kananan hukumomi 774 na Najeriya tare da sanya ido ta hanyar bayanan NIMS da ake duba kai tsaye.
Kakaki24 ta tattaro cewa wannan shi ne karo na farko da NMEC ta gudanar da irin wannan babban aikin tattara bayanan wadanda Basa zuwa makaranta tun bayan binciken shekarar 2010. Wannan ya nuna an samu sabuwar kudirin gwamnati na cike gibi a bangaren ilimi da karatun manya. Za a gudanar da zangon farko na karatun ne cikin watanni shida zuwa tara, gwargwadon yadda ake samun lokutan karatu a yankuna.
Shirin ya samu goyon bayan Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da Hukumar UBEC. Haka kuma, daraktan shirye-shiryen NMEC, Mista Samuel Aziba, ya bayyana cewa horon zai bai wa masu tattara bayanai damar amfani da na’urorin zamani. Matakin gwaji zai fara ne a wurare hudu na FCT kafin a bazar da shi a fadin kasar. Najeriya na da kimanin manya miliyan 30 da ba su iya karatu ba – al’amari da ya sa wannan shiri ya zama na gaggawa.
