Featured
Akwai Yiwuwar Tinubu Zai Naɗa Christopher Musa a Matsayin Sabon Ministan Tsaro
Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar ya ajiye aikinsa saboda dalilan lafiya, lamarin da ya tilasta wa Shugaba Bola Tinubu fara shirin sauya mukamin cikin gaggawa. Badaru ya sanar da murabus dinsa ne ta wata wasika da ya aika wa shugaban kasa, wacce ta fara aiki nan take.
A cewar sanarwar da mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya amince da murabus din tare da mika godiya bisa gudunmawar Badaru. Ana sa ran shugaban zai tura sunan wanda zai maye gurbin tsohon ministan ga majalisar dattawa cikin wannan makon.
Rahotanni sun nuna cewa murabus din ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke fama da karuwar matsalar tsaro, lamarin da ya sa Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasa tare da daukar matakan gaggawa. A cikin matakan har da daukar karin ’yan sanda 20,000 da tura ’yan sa kai na kare dazuka da tsare ibadodi a wuraren da ake ganin suna cikin hadari. Kakaki24 ta tattaro cewa akwai masu sukar Badaru tun farko suna ganin bai dace da mukamin ba.
Kafin bayyana murabus din, Shugaba Tinubu ya gana da tsohon babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa (ritaya), a fadar shugaban kasa da misalin karfe 7:03 na yamma. Ganawar ta janyo cece-kuce cewa watakila Musa na cikin wadanda ake duba domin maye gurbin kujerar Ministan Tsaro.
