Connect with us

Featured

An Kama Sojojin Da Suka Yi Yunƙurin Juyin Mulki a Benin

Rahotanni daga Jamhuriyar Benin sun tabbatar da cewa an kama sojoji da dama bayan wani yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba da safiyar Lahadi. Majiyoyi sun ce an damke waɗanda ake zargi da jagorantar yunkurin, ciki har da tsohon soja da aka kora a baya. Sojoji 13 ne aka ce sun shiga gidan talabijin domin sanar da tsige Shugaba Patrice Talon kafin jami’an tsaro su mamaye wurin.

 

A cewar Ministan Harkokin Cikin Gida, Alassane Seidou, wanda ya bayyana a gidan talabijin, dakarun gwamnati sun yi nasarar murƙushe yunkurin nan take bayan da ‘yan tawaye suka bayyana suna ikirarin karɓar mulki. Ya ce yunkurin ya fito ne daga ƴan tsirarun sojoji masu neman tada zaune tsaye a Benin ba tare da samun goyon bayan rundunar tsaro ba.

 

Majiyar gwamnatin Benin ta shaida wa BBC cewa Shugaba Talon yana cikin ƙoshin lafiya, kuma babu wani barazana da ta rutsa da lafiyarsa. A cewar jami’an diflomasiyyar Faransa, rahotannin farko da suka nuna cewa shugaban ya nemi mafaka a ofishin jakadancin Faransa ba gaskiya ba ne, lamarin da ya ƙara fayyace gaskiyar abin da ya faru, kamar yadda Kakaki24 ta tattara.

 

Yanzu haka an ci gaba da tsaurara matakan tsaro a birnin Cotonou, tare da hukumomi na ƙoƙarin gano ko akwai sauran masu hannu a cikin yunkurin da ya gaza cimma nasara. Gwamnatin Benin na cigaba da bai wa jama’a tabbacin cewa lamarin ya ƙarƙare, kuma an dawo da doka da oda a fadin ƙasar.

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet