Connect with us

Featured

Daga Yanzu Ƴan Najeriya Ba Za Su Iya Yin Shiri Da Daddare Kai Tsaye Ba – TikTok

Shahararriyar manhajar TikTok ta sanar da takaita damar yin LIVE ga masu amfani da ita a Najeriya tsakanin ƙarfe 11 na dare zuwa 5 na safe, inda ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na binciken tsaro domin kare al’ummar ta. TikTok ta aika sanarwa cikin manhajar tana bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne don tabbatar da cewa dandalin ya ci gaba da kasancewa cikin aminci da kariya.

Rahotanni sun nuna cewa daga misalin ƙarfe 11 na dare, asusun masu amfani da suka saba yin LIVE ya fara nuna “No Access”, kuma ba su iya kallo ko shiga irin waɗannan shirye-shirye ko daga wata ƙasa ba. Wannan mataki ya fi shafar masu dauke da mabiya fiye da 1,000, wato waɗanda ke da damar yin LIVE. Duk da cikas ɗin, TikTok ta tabbatar cewa ba a shafi kuɗaɗen da masu LIVE ke samu ba, domin asusun kuɗinsu ya kasance yadda yake.

Kakaki24 ta tattaro cewa wannan takaitawar ta janyo tattaunawa mai zafi a dandalin sada zumunta da safiyar Litinin, bayan dawo da damar yin LIVE. Masu amfani da dama sun nuna damuwa ganin cewa dare ne lokacin da ake samun mafi yawan masu kallo a Najeriya, musamman masu watsa wasanni, nishadi, hira da kuma gwagwarmayar samun kyaututtukan LIVE.

TikTok ta bayyana a taron West Africa Safety Summit da aka gudanar a Dakar cewa a watanni na biyu na 2025 ta dauki mataki kan fiye da 2.3m na shirye-shiryen LIVE a duniya da kuma fiye da 1m na masu yin LIVE saboda karya ka’idojin monetisation. A Najeriya kadai, an dakatar da 49,512 na shirye-shiryen LIVE a wannan lokaci, sannan an goge fiye da 3.7m na bidiyo tsakanin Afrilu da Yuni saboda take doka, mafi yawansu kafin ko an fara kallo.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet