Connect with us

Featured

NDLEA Ta Gargaɗi Ɗalibai Kan Shan Miyagun Ƙwayoyi

Ƙungiyoyin HEPPWAS tare da hadin gwiwar NDLEA, Rotary Club na Yenagoa City Centre da Damaris Hotel & Suites, sun gudanar da wayar-da-kai ga daliban Government Secondary School, Obogoro, kan illolin shan miyagun kwayoyi ga ƙwaƙwalwa. Fiye da dalibai 100 ne suka amfana, inda aka yi wa taron take da suna: “Sensitisation on Substance Uses and Its Impacts on Youths’ Brain.”

Shugabar HEPPWAS, Farfesa Izebeloko Jack Ibe, ta yi bayani dalla-dalla kan yadda kwayoyi ke lalata ƙwayoyin kwakwalwa wadanda ba sa samun sabuntawa idan sun bace. Ta ja hankalin dalibai da kada matsalolin rayuwa su karkatar da su zuwa bin miyagun halaye. NDLEA ta kara bayyana wasu daga cikin muggan kwayoyi da ake yawan amfani da su, ciki har da ice, fentanyl, cannabis da ogogoro, wadanda ke haifar da rikice-rikice da tashin hankali a cikin al’umma.

A jawabin da Kakaki24 ta tattara, jami’an ƙungiyoyi daban-daban daga Obogoro, ciki har da Dr. Pawei Igodo da Mr. Ben Ibe, sun bayyana cewa yawaitar shaye-shaye na daga cikin manyan dalilan rashin tsaro da karuwar matsalolin zamantakewa a fadin kasar. Sun jaddada bukatar matasa su mai da hankali kan karatu, tare da gujewa duk wani lamari da zai lalata musu makoma.

Makarantar ta nuna godiya ga masu daukar nauyin taron, inda Principal, Mrs. Dick Agbeyen, ta ce ya dace gwamnati ta saka darasin illolin shaye-shaye a manhajar makarantu. Wani dalibi, Awake Dufaye Daniel, ya ce ya samu sabon ilimi game da yadda kwayoyi ke lalata kwakwalwa da rayuwar mutum baki ɗaya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet