Connect with us

Featured

An Shigo Da Motoci Na Fiye Da Naira Tiriliyan 1 Najeriya Cikin Watanni 9

Shigo da motocin fasinja zuwa Najeriya ya samu gagarumar farfaɗowa a shekarar 2025, inda adadin kuɗin shigo da su ya kai ₦1.01 tiriliyan a watanni tara na farkon shekarar, a cewar alkaluman Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS). Wannan adadi ya fi na irin wannan lokaci a 2024 da ₦113.15 biliyan, wanda ke nuna ƙarin kusan kashi 12.7 cikin 100, bayan raguwar da aka samu a baya sakamakon rikicin canjin kuɗaɗen waje da tsadar shigo da kaya.

Rahoton ya nuna cewa duk da raguwar da aka samu a zangon farko da na biyu na 2025, inda masu shigo da motoci ke ci gaba da fuskantar matsin lambar rashin tabbas a kasuwar canjin kuɗi, sai dai a zangon uku ne aka samu gagarumar tashin gwauron zabo. Tsakanin Yuli da Satumba 2025, darajar shigo da motoci ta haura zuwa ₦527.98 biliyan, ƙaruwa da kusan kashi 45 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, abin da ya share dukkan gibin da aka samu a farkon shekarar.

Masana tattalin arziƙi sun danganta wannan farfaɗowa da kwanciyar hankalin Naira da sauƙaƙen samun dalar Amurka a zangon uku na 2025. Sun ce tsayayyen canjin kuɗi, ƙarin kuɗaɗen man fetur, da tsoma bakin Babban Bankin Najeriya (CBN) sun ƙarfafa gwiwar ‘yan kasuwa. Amurka ta kasance babbar ƙasar da Najeriya ke shigo da motoci daga gare ta, inda ta kai sama da kashi 41 cikin 100 na jimillar shigo da motocin fasinja, yayin da shugabannin dillalan kaya ke cewa sauƙaƙƙen haraji da sabbin hanyoyin tantance harajin kwastam sun taimaka wajen ƙara yawan motocin da ke shigowa ƙasar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet