Connect with us

Featured

One Kano Agenda: Durƙushewar Masana’antu Ne Ke Haddasa Koma Bayan Kasuwanci a Kano — Bash M Bash

Fitaccen ɗan jarida kuma mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum, Bash M Bash, ya bayyana cewa durƙushewar harkokin masana’antu a Kano, shi ne ke haddasa koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arzikin jihar.

Bash M Bash ya ce rashin ayyukan masana’antu ya janyo koma baya ga harkokin sana’o’i da kasuwanci, tare da rage guraben ayyukan yi da kuma shigar kuɗaɗen shiga a jihar. A cewarsa, idan har ana son Kano ta dawo matsayinta na cibiyar kasuwanci a Arewa da ma Najeriya baki ɗaya, wajibi ne a farfado da masana’antu.

Ya yi kira ga manyan attajiran Kano, musamman Alhaji Aliko Dangote da Abdulsamad Rabiu (BUA), da su tashi tsaye wajen farfaɗo da tsofaffin masana’antu da ke yankunan Sharada, Challawa da Dakata, domin su taka rawar gani wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Bash M Bash ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis 18 ga Disamba, 2025, yayin wani taron yini biyu da ƙungiyar One Kano Agenda ta shirya, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu (KHAIRUN), da ke Kofar Gadon Kaya a cikin birnin Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet