Connect with us

Featured

Wani Likita Ya Cirewa Mara Lafiya Ƙoda Bisa Kuskure

Gwamnatin Jihar Ekiti ta kori wani likita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Ekiti (EKSUTH), Ado-Ekiti, bisa zargin yin tiyata da ta jawo cire kodar wani mara lafiya, Joshua Afolayan, ba tare da cikakken izini ba. Haka kuma, gwamnatin ta dakatar da dukkan mambobin tawagar tiyatar da suka halarci aikin na tsawon wata guda domin ƙarin bincike da matakan ladabtarwa.

Afolayan ya bayyana cewa ya je asibitin ne sakamakon haɗari, inda gwaje-gwaje suka nuna cewa ɗaya daga cikin kododinsa na aiki, ɗaya kuma ba ya aiki. Sai dai bayan an yi masa tiyata, ya gano cewa kodar da ke aiki ita ce aka cire, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da zargi a cikin al’umma.

Bayan haka, gwamnatin jihar ta kafa kwamitin bincike mai mutum bakwai ƙarƙashin jagorancin Farfesa Francis Faduyile, wanda ya kammala cewa lamarin matsalar tiyata ce, ba satar gabobi don tsafi ba.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Ekiti, Dokta Oyebanji Filani, ya ce rahoton kwamitin ya tabbatar da tauye ƙa’idojin aiki, inda aka yanke shawarar korar likitan da ya jagoranci aikin nan take, tare da dakatar da sauran tawagar tiyatar na wata guda. Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin dasa sabuwar koda ga Afolayan tare da kula da lafiyarsa bayan tiyata na tsawon shekaru biyu, yayin da za a aiwatar da gyare-gyare a asibitin domin ƙarfafa tsaro, ɗabi’a da amincewar jama’a ga tsarin kiwon lafiyar jihar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet