Featured
Ghana Ta Kori Ƴan Najeriya 42 Saboda Zargin Karuwanci

Gwamnatin yankin Ashanti a ƙasar Ghana ta kori ’yan Najeriya 42 bayan hukuncin kotuna kan zargin karuwanci, damfara da wasu laifuka masu nasaba da haka. Ministan yankin Ashanti, Frank Amoakohene, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a Facebook ranar 18 ga Disamba, 2025, inda ya ce matakin ya biyo bayan shari’o’in da suka shafi Q-Net da sauran ayyukan aikata laifi.
A cewarsa, ba ’yan Najeriya kaɗai aka kora ba, domin matakin ya shafi ’yan Kamaru 13, ’yan Ivory Coast 3, ’yan Burkina Faso 3 da ’yan Benin 7, wanda ya kai jimillar ’yan Afirka 68 da kotuna suka bayar da umarnin korar su. Amoakohene ya yabawa Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ghana bisa jajircewa da ƙwarewa wajen aiwatar da dokokin ƙasa tare da mutunta ’yancin ɗan Adam da bin doka da oda.
Korarrun ’yan Najeriya sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rahotannin tsauraran matakai kan ’yan Najeriya a ƙasashen waje. A ƙarshen watan Nuwamba, rahotanni sun nuna cewa fiye da ’yan Najeriya 50 sun faɗa hannun hukuma a Indiya bisa zargin hannu a wata babbar hanyar safarar miyagun ƙwayoyi da wanke kuɗi, lamarin da ke ƙara janyo hankalin hukumomi a ƙasashe daban-daban kan ayyukan wasu ’yan ƙasashen waje.