Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙudiri Aniyar Fara Ƙera Motoci Masu Sauƙi a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada kudirinta na bunƙasa kera motoci a cikin gida domin rage dogaro da shigo da tsofaffin motoci daga ƙasashen waje. Ministar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, ta bayyana hakan ne, inda ta ce gwamnati na shirin tabbatar da samuwar sabbin motoci masu araha da aka kera a Najeriya nan da shekarar 2026, ta hanyar ƙarfafa masana’antu da faɗaɗa rancen kuɗi ga masu saye.

 

Ministar ta yi wannan jawabi ne yayin wata ziyarar aiki da ta kai masana’antar Elizade JAC Motors a Lagos, inda ta yaba da ingantattun layukan haɗa motoci da kuma tsarin zamani da kamfanin ya samar. Ta bayyana faɗaɗa masana’antar a matsayin alamar amincewa da tattalin arzikin Najeriya, tare da jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta ci gaba da goyon bayan masu zuba jari na cikin gida domin samar wa ‘yan ƙasa motoci masu inganci, lafiya da araha, maimakon shigo da tsofaffin motoci marasa tabbas.

 

A nasa bangaren, shugabannin Elizade JAC Autoland sun ce babban dalilin da ke sa mutane komawa tsofaffin motoci shi ne tsadar sabbi, amma kamfanin na shirin rage farashi tare da haɗa kunshin gyara da kulawa domin sauƙaƙa wa masu saye a 2026. Kakaki24 ta ruwaito cewa gwamnati na kuma ƙarfafa tsarin rancen kuɗi ga ‘yan ƙasa, domin haɓaka sayen kayayyakin da aka kera a gida, wanda ake sa ran zai inganta rayuwar al’umma tare da bunƙasa tattalin arziki gaba ɗaya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet