Featured
Gwamnatin Tarayya Ta Fara Kulle Asusun Ƴan Ta’adda a Kafafen Sada Zumunta
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, hukumomin tsaron Najeriya sun ƙara ƙaimi wajen haɗa kai da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta, domin gano tare da goge asusun da ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka ke amfani da su, wajen yaɗa ayyukansu da kuma tara kuɗaɗe. Wannan bayani ya fito ne a ranar Talata, 23 ga Disambar 2025, a Abuja, yayin taron ƙarshen shekara na Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC).
Daraktan Janar na NCTC, Manjo Janar Adamu Laka, ya ce kafafen sada zumunta irin su TikTok, Facebook, Instagram, Snapchat da X, sun taɓa zama dandamali da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen nuna ganima, yaɗa farfaganda da sadarwa da magoya bayansu. Ya bayyana cewa, an yi taruka da dama da waɗannan kamfanoni, inda aka goge dubban asusu da ke barazana ga tsaron ƙasa, lamarin da ya taimaka wajen dakile nuna ayyukan ‘yan fashi da sace-sace kai tsaye a intanet.
Laka ya kuma ƙara da cewa, kuɗin fansa na daga cikin manyan hanyoyin da ake bi wajen tallafa wa ta’addanci, inda ake amfani da asusun POS wajen ɓoye sawun kuɗaɗen. Ya kuma tabbatar da cewa, hukumomin tsaro na ƙara bibiyar waɗannan hanyoyi, tare da cafke masu hannu da shuni da kwace kadarori, yana mai jaddada cewa Najeriya za ta ƙara ƙarfafa matakan yaki da ta’addanci, musamman a fannin dijital, a shekarar 2026 duk da ƙalubalen tsaro a yankin Sahel.
