Featured
Ƙungiyar Lauyoyi Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Aiwatar Da Sabbin Dokokin Haraji
Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji, tana mai cewa dole ne a fara dawo da amincewar jama’a kafin a fara aiwatar da su. Shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe, SAN, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 23 ga Disamba, 2025, inda ya nuna damuwa kan rikice-rikicen da suka taso game da sahihanci, gaskiya da amincin tsarin dokokin da Majalisar Dokoki ta kasa ta bi wajen zartar da dokokin.
Kungiyar ta nuna cewa zargin da dan Majalisar Wakilai, Hon.Abdulsammad Dasuki (PDP, Sokoto), ya yi na cewa akwai banbanci tsakanin dokokin harajin da aka amince da su a Majalisa da kuma wadanda aka wallafa a hukumance, ya kara tayar da hankula. Tun bayan wannan zargi, jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula da wasu ‘yan majalisa sun fara kira da a dakatar da dokokin, suna nuna cewa akwai kura-kurai da ba a warware ba a cikinsu.
NBA ta jaddada cewa dokoki masu girman tasiri irin wadannan dole ne su fito ta hanyoyi masu gaskiya da rikon amana. Ta bukaci dukkan hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta daukar mataki domin bincike a bude, domin kare tsarin mulki, tabbatar da kwanciyar tattalin arziki da kuma mutunta doka. Kungiyar ta gargadi cewa rashin tabbas a doka na iya girgiza harkokin kasuwanci, rage amincewar masu zuba jari, tare da barazana ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya.
